Yau wani rana
Anyi haihuwa an koma kuka
Kana A/c, kana neman fanka
Matan Mallam a wajan boka
Dan Adam kake, mutane ke fadin halinka
Kankanin lokaci Nigeria zata zamo Amurka

Yau wani rana
An kawo wuta ba'a shela
Sallah an manta da alwala
Fara cin abinci, babu Bismilla
Tela a sahun farko ya gama dinkin sallah
Tunanin duniya maisa amanta da Al'qibla

Yau wani rana
Angama siyasa babu gaba
Yaro da furfura, yazamo babba
An koma satan waya a makabarta
Musulmi ya koma addinin Kirista
Wajan Janaiza an koma daukan hotona
An ajiye Kabilanci, anzamo abokan juna
Wajan ibada ya koma wajan gulma
Mace yar shekara biyar dauke da mama

Yau wani rana
Masu tsaro ba ruwan su da karfan cin hanci
Masu kudi na gudun shuwa gabanci
Talaka yazama mai kudi ya manta da talauci
Turaran gawa, ya zamo turan kamshi
Shuwa gabanni ansa Allah, an bar wawanci

Yau wani rana
Mata anyi wanka babu kwalliya
Kani yazamo yaya saboda sanin ya kamata
Shaye shaye mai sa akira dare safiya
Zafin haihuwa maisa amanta soyayya
Daukan ciki yazama ado, an daina jin kunya
Barku ku, nace ku huta lafiya