Indai ina raye
Har idan muna raye
Mun farka, garin kuma ya waye
Kada muyi wasa da iyaye
Mu fadi, tashi atare
Inada abokanai da kawaye
Farin ciki kullan, Ida nuwana babu hawaye
Bakake muke so, ba ruwan da farare
Garina Kano, kauyukana Sumaila da Karaye

Indai ina raye
Kirani da sunana, banison ranka yi dade
Saukin kai gareni banida da girman kai
Karatu baya albarka idan ba'a girmama Mallamai
Allah! kareni, karemu da sharrin Shaidanu, da mugayam mutane
Kowa na mune, babu ruwan da kayan maye

Indai ina raye
Zamuyi ziyara a garuwwa
Mu koya ya fewa
Muzamo masu kishin kasarmu a Arewa
Ku cigaba da hutawa
late Sardauna da Tafawa Balewa